Tsakanin 15 da 20 na watan Yuni, an samu ƙaruwar yawaitar faɗan daba a anguwannin sharaɗa, Ja’in da Dala da ke cikin birnin jihar Kano. A dalilin haka ne, rundunar ƴan sandan jihar Kano suka ɗau alwashin ganin sun yi ƙokari wajen ganin hakan bai cigaba ba.
A anguwar Sharaɗa-Ja’in, wani hari da aka kaiwa shugaban yan vigilante Muktar Garba, yayi sanadiyar rasa ransa. Manyan waɗanda ake zargi, Umar Shaibu da Umar Kabiru suna hannun yan sanda. Domin sune ake da zargin ke yawan tada hankula a wannan anguwan.
Haka ma a anguwar Dala, faɗan daban yayi sanadiyar mutuwar wani wanda ake kira da Bukari Tijjani. Waɗanda ake zargi sun haɗa da, Adamu Ado, Ibrahim Ahmad da kuma Abubakar Abdullahi duk suna hannun hukuma.
A yayin wani atisaye tsakanin 15 da 20 watan Yuni, an yi nasarar cafke yan daba da dama, tare da muggan makaman da suke amfani dasu.
