Daga RABIU SANUSI a Kano
Kamfanin Dangote Cement Plc, Gboko Plant, ya fara gudanar da Makon ɗorewar Cigaba na 2025, wani shiri na shekara-shekara da ke nuni da jajircewar kamfanin wajen kare muhalli, kula da al’umma, da kuma haɓaka tattalin arziki.
A jawabinsa yayin ƙaddamar da shirin, Daraktan Kamfanin, Injiniya Abhijit Dutta, ya bayyana cewa ɗorewar cigaba na nufin “cika buƙatun yau ba tare da tauye damar al’umman gaba wajen cika nasu buƙatun ba.”
Ya ce, a ɓangaren ƙera siminti, ɗorewar cigaba yana nufin kiyaye daidaito tsakanin mutane, muhalli da riba.
Taken makon ɗorewar cigaba na bana ya mayar da hankali ne kan murnar irin gudunmawar ma’aikata wajen tabbatar da ingantaccen aiki da dawwamammen samar da kayayyaki a DCP Gboko, tare da girmama masu bada kaya, masu kwangila da abokan hulɗa da suka taimaka wajen cimma wannan nasara.
An ƙaddamar da makon ne a hukumance a DCP Gboko ta hannun Daraktan kamfanin.
Injiniya Dutta ya jaddada muhimmancin kiyaye ginshiƙan ɗorewar cigaba na mutane – Muhalli -Riba, yana mai cewa: “Yana da muhimmanci mu ci gaba da kare nasarorin da muka samu a DCP Gboko. Mun rage tsaiko a masana’antar kuma mun samu nasara wajen aiwatar da dabarun mayar da shara zuwa abin amfani.
A halin yanzu, muna aiwatar da tsarin 5S a sassan masana’antar. Wannan nasara ta samu ne saboda jajircewar ma’aikatanmu da abokan hulɗa.”
Ya kuma bayyana cewa masana’antar Gboko ta kuduri aniyar aiwatar da manufofin Majalisar ɗinkin Duniya na ɗorewar Cigaba (UN SDGs), musamman a ɓangaren Kare Muhalli, DANGCIRCULAR, da Rage Fitar Da Hayaƙi ta hanyoyi na kimiyya da halitta, irin su dashe (afforestation).
Ya ce, DCP Gboko ta fara amfani da ɓawon shinkafa da bawon kwakwa a matsayin makamashi madadin dizal.
A nasa ɓangaren, Shugaban Sashen Kula da Ma’aikata, Malam Abubakar Abdulkareem, ya jaddada cewa ƙa’idojin ESG (Muhalli, Al’umma da Gudanarwa) sun zama wajibi a harkokin kasuwanci na zamani.
“ESG ya zama muhimmin ginshiƙi a kowace kasuwanci. DCP Gboko ta nuna ci gaba da gaskiya ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar cigaban al’umma mai darajar miliyoyin daloli (CDA), ta aiwatar da shirye-shiryen tallafawa manoma a yankunan da ke ƙarƙashinta, gina rijiyoyi, da gudanar da shirye-shiryen karfafa mata da matasa,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Dole mu ci gaba da nuna ƙwarewa da sadaukarwa ta hanyar aiki ‘The ɗangote Way.’”
An fara Makon ɗorewar Cigaba da taron tafiyar lafiya mai taken “Power-in-Blue: Tafiyar Lafiya ta Ma’aikata na kilomita 10.”
An jagoranci tafiyar ne ta Daraktan Kamfanin, Inj. Dutta, tare da Malam Abubakar Abdulkareem (Shugaban Ma’aikata da Gudanarwa) da Malam Olusegun Orebanjo (Shugaban Harkokin Kuɗi).
Ma’aikatan DCP Gboko da Dangote Cement Transport sun halarta, inda suka yi tafiya daga masana’antar zuwa Amua-Tyeku a Gboko sannan suka dawo. Jami’an FRSC Gboko da ’Yan Sandan Gboko Diɓision sun bayar da goyon baya wajen tabbatar da tsaro.
Al’ummar yankin sun fito cikin farin ciki suna taya ma’aikatan kamfanin murna, wanda ya nuna haɗin kai da ƙarfafa Manufar SDG ta 3 Lafiya da Walwala.
An kammala bikin da wasa na ɓolleyball tsakanin DCP Gboko da ɗangote Cement Transport (DCT), inda ƙungiyar DCP Gboko ta haɗa maza da mata, yayin da DCT ta fito da ƙungiyar maza.
Wasan ya kasance cike da nishadi da gasa, kuma a ƙarshe, ɗangote Cement Transport (DCT) ta lashe wasan da ci 2–0.
Taken Makon ɗorewar Cigaba na bana shine: “Sustainable Progress: Celebrating Growth & Partnerships” wato ɗorewar Cigaba: Murnar Haɓaka da Haɗin Kai, wanda ya yi daidai da manufofin Majalisar ɗinkin Duniya na SDG 3 (Lafiya da Walwala), 9 (Masana’antu, ƙirƙira da Gine-gine), 13 (Kare Muhalli), da 17 (Haɗin Kai Domin Cimma Manufofi).
