Muna zaune lafiya da sauran ƙabilu mazauna Jihar Legas – Sarkin Hausawan Imota

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Sarkin Hausawan karamar hukumar Imota da ke yankin Ikorodu a jihar Legas, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana cewa al’ummar Hausawa mazauna yankin Imota da sauran ƙabilun Arewacin Nijeriya suna zaune lafiya da sauran kabilu mazauna Legas da kewaye.

Alhaji Ibrahim Haruna, wanda asalinsa daga karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano ne, ya bayyana haka ne a hirarsa da Jaridar Blueprint Manhaja a Legas, inda ya ce tun shekaru da dama da suka gabata ake samun zaman lafiya da jituwa tsakaninsu da sauran al’ummomin jihar.

Ya ce tun bayan rikicin da aka taba samu tsakanin Hausawa da ƙungiyar OPC shekaru da suka gabata, yanzu babu wata matsala ko tashin hankali a tsakanin ƙabilun da ke zaune a Imota da ma sauran sassan Legas. A cewarsa, mazauna yankin suna gudanar da harkokin kasuwanci da rayuwar yau da kullum cikin lumana da fahimtar juna.

Sarkin ya ƙara da cewa, “A halin yanzu muna da kyakkyawar dangantaka da makwabta, musamman ‘yan ƙabilar Yarbawa da sauran jama’a. Muna yin kasuwanci tare, muna girmama juna, kuma muna bin dokokin gwamnati domin ci gaban kowa da kowa.”

Har ila yau, ya yi kira ga Hausawa da Yarbawa mazauna yankin Imota da sauran sassan Legas da su ci gaba da zama lafiya, su hada kawunansu, tare da guje wa duk wani abin da zai kawo sabani ko rikici a tsakaninsu.

Alhaji Ibrahim Haruna ya kuma jinjinawa Gwamnatin jihar Legas, karkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu, bisa irin ayyukan ci gaba da ta ke aiwatarwa a fadin jihar. Ya ce gwamnan ya zama abin koyi ga sauran shugabanni a fannin cika alkawura da aiwatar da manufofin da ke amfanar jama’a.

A cewar sa, “Gwamna Sanwo-Olu yana nuna irin nagartaccen shugabanci wanda ya kamata sauran gwamnoni da ‘yan siyasa su yi koyi da shi wajen hidimtawa al’umma da gaskiya da amana.”

Daga ƙarshe, Sarkin Hausawan Imota ya yi addu’a ga kasar Nijeriya baki daya, yana rokon Allah Ya ci gaba da zaunar da ƙasar lafiya, Ya kuma ƙarawa shugabanni basira da jagoranci nagari domin ci gaban ƙasa.

By ukarofi