Kamfanin Sin ya samar wa ɗaliban firamaren Habasha dake fama da talauci wasu kayayyakin karatu

Daga CMG HAUSA

A ranar 9 ga wata, reshen kamfanin CCECC na ƙasar Sin dake ƙasar Habasha, ya samar wa ɗaliban firamaren kasar masu fama da talauci 100 dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin ƙasar wasu kayayyakin karatu.

Rahotannin sun bayyana cewa, kayayyakin karatun da kamfanin ƙasar Sin ya samar sun haɗa biro da litattafai, da jakar adana litattafai da sauransu, kana kamfanin ya samar wa ɗaliban wasu kayayyakin wasan motsa jiki ciki har da teburin wasan ƙwallon tebur, da ƙwallon tebur.

Mataimakin shugaban hukumar ba da ilmi ta birnin Addis Ababa Ademasu Dechasa, ya bayyana yayin bikin miƙa kayayyakin cewa, gwamnatin ƙasar Sin da jama’ar ƙasar, sun samar da goyon baya matuka ga ci gaban ƙasarsa ta Habasha, musamman ma wajen ba da ilmi, ya kuma nuna fatan cewa, ƙasar Sin za ta ci gaba da samar da tallafin a fannin.

A nasa ɓangaren kuma, babban manajan kamfanin CCECC na ƙasar Sin reshen ƙasar Habasha Zheng Chongfeng ya bayyana cewa, aikin ba da ilmi yana da muhimmanci ƙwarai ga ci gaban kasa, kuma kamfaninsa yana samar da tallafi wajen ba da ilmi ga Habasha ne, bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa