Shugabancin Nijeriya: Tinubu ya gana da gwamnonin APC a Abuja

Daga BAHIR ISAH

Jigo a jam’iyyar APC kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata ganawa tare da gwamnonin APC jiya Litinin a masaukin baƙi na jihar Kebbi da ke Abuja.

Tinubu ya gana da gwamnonin ne wasu sa’o’i bayan da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wa duniya aniyarsa ta takarar shugaban ƙasa a 2023.

Shi ma dai Osinbajo sai da ya yi wata ganawa da wasu gwamnoni da yammacin Lahadin da ta gabata kafin washegari ya bayyanar da ƙudirinsa na sha’awar takarar kujerar Shugaban Ƙasa,

Kimanin gwamnonin APC su 17 ne Tinubu ya gana da su, da suka haɗa da: Abubakar Bagudu na Kebbi, Nasir El-Rufai na Kaduna, Bababjide Sanwo-Olu na Legas, Abdullahi Ganduje na Kano, Gboyega Oyetola na Osun, Mai Mala Binu na Yobe, Simon Lalong na Filato, Abubakar Badaru na Jigawa, Dapo Abiodun na Ogun, Abdullahi A. Sule na Nasarawa da sauransu.

Yayin ganawar tasu

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita, Sakataren Labarai ga Gwamnan Legas, Gboyega Akosile Tinubu da gwamnonin sun tattauna muhimman batutuwa a tsakaninsu.