Kane ya shiga jerin ’yan wasan Ingila 10 da suka doka wa ƙasar wasanni 100

Spread the love

Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya shiga jerin ‘yan wasa na 10 a tarihi da suka dokawa ƙasar wasa sau 100 yayin wasan da Three Lions suka kara da Finland a ranar Talata ƙarƙashin gasar Nations League, wasan da ya gudana a Wembley da ke Landan. 

Kane mai shekaru 31 a shekarar 2015 ya fara dokawa Ingila wasa inda zuwa yanzu ya haska a wasanni 100 tare da zura ƙwallaye 66.

Kai tsaye ɗan wasan gaban na Bayern Munich zai bi sahun Wayne Rooney wanda a watan Nuwamban 2014 ya cika wasanni 100 da ya dokawa Ingila, ko da ya ke bai yi ritaya ba sai da ya dokawa kasar ta shi wasanni 120 wanda ya mayar da shi ɗan wasa na biyu mafi dokawa Ingila wasanni, ƙasa da mai tsaron raga Peter Shilton wanda ya dokawa Ingila wasanni 125.

Sauran ‘yan wasan Ingila da suka dokawa ƙasar wasanni 100 zuwa sama sun ƙunshi Daɓid Beckham wanda ya doka wasanni 115 kana Steɓen Gerrard da wasanni 114 sai Bobby Moore da wasanni 108 kana Ashley Cole da wasa 107.

Sauran sun haɗa da Bobby Charlton mai wasanni 106, kana Frank Lampard da wasanni 106 shi ma tukuna Billy Wright da wasanni 105.

Kane a zantawarsa kafin wasan, ya ce ko shakka babu jadawalin ‘yan wasan Ingila da suka doka wasanni 100 zuwa sama na aunshe na zaƙaƙurai da tarihin ƙwallo ba zai mantawa da su ba, don haka abin alfahari ne yadda ya samu kansa a wannan jerin.

A cewar Kane yanzu abin da ya rage masa shi ne ganin ya zurawa ƙasar shi ƙwallaye 100 kamar yadda yanzu ya ke shirin doka wasa na 100 ta yadda zai riƙa waiwayen tarihin da ya kafa bayan ritaya.

By ukarofi