Man United ta yi asarar yuro miliyan 113.2 a 2023-24

Spread the love

Kungiyar Manchester United ta sanar da yin asarar yuro miliyan 113.2 a kakar 2023/24 zuwa ƙarshen watan Yuni.

Hakan ya biyo bayan hasarar yuro miliyan 28.7 a 2022-23 da kuma yuro miliyan 115.5m a 2021-22, kenan ta faɗi kasuwanci a kaka biyar da ya kai fiye da yuro miliyan 370.

Sai dai duk da haka, United na ƙoƙarin kada ta yi laifin karya dokar kashe kuɗi daidai samu ta Premier League da kan kwashe maki, idan ƙungiya ta karya ƙa’ida.

A dokar ta tanadi cewar bai kamata ƙungiya ta yi hasarar yuro miliyan 105 cikin kaka uku ba, inda a bara aka hukuntan Eɓerton da Nottingham Forest, waɗanda aka kwashe masu maki.

A watan Yuli, United ta sanar da cewar za ta rage ma’aikata 250 a wani tsari na kara bunƙasa ƙungiyar.

United ta ce tana sa ran samun kuɗi yurp miliyan 30 da yuro miliyan 35 cikin shekara biyu tun daga 2025.

Kungiyar Old Trafford, wadda aka daɗe ana bin bashin yuro miliyan 496.52 ta ƙara da cewa tana sa ran samun yuro miliyan 650, yayin da albashi zai karu da kaso 10 cikin 100 wato yuro miliyan 364.7.

United, wadda za ta kara a Europa League a bana, sakamakon lashe FA Cup a bara, ta ci wasa ɗaya aka doke ta biyu a Premier League ta bana kawo yanzu.

Kungiyar ta ɗauki ’yan wasa kan fara kakar nan da ya haɗa da Manuel Ugarte da Joshua Zirkzee da Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Noussair Mazraoui.

By ukarofi