Ambaliya ta kashe mutum 24 a Bauchi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi ta tabbatar da cewa kawo yanzu mutane 24 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ake ci gaba da yi a ƙananan hukumomi 16 na jihar.

An kuma samu rahotannin asarar dukiya da ta kai sama da naira biliyan 22.

Majalisar ta bayyana cewa ta kafa wani kwamiti domin tantance irin ɓarnar da bala’in ya janyo.

Da take magana da manema labarai bayan taron majalisar, kwamishinar kula da ayyukan jin ƙai da kula da bala’o’i, Hajara Wanka, ta bayyana cewa ma’aikatar na ci gaba da tattara rahotonta kan ɓarnar da ambaliyar ta yi.

Ta ce, “Daga rahotonnin da aka tattara, ya zuwa yanzu mutum 24 sun rasa rayukansu, 163 kuma sun samu raunuka, a kananan hukumomi 16.”

Ta ƙara da cewa ambaliyar ta shafi mutane 122,330 da dabbobi 11,183 inda gidaje 52,000 suka ruguje. Ta kuma datse manyan tituna 12, tare da lalata turakun wutar lantarki 178.

Kwamishinar ta kuma tabbatar da cewa majalisar ta amince da sakin kuɗaɗe don gyara gine-ginen da suka lalace, da suka haɗa da magudanan ruwa da tituna da kuma makarantu.

By ukarofi