Yadda Chelsea ta raina ni – Osimhen

Spread the love

Ɗan wasan Nijeriya, Victor Osimhen, ya bayyana dalilin janye shirin sauya sheƙarsa zuwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea a bazara.

A wata tattaunawa ta musamman tare da mai watsa shirye-shiryen wasanni na Arise Tɓ, Aaron Akerejola, ɗan shekaru 25, ya bayyana wasu dalilai kan ƙin tafiyarsa filin wasa na Diego Armando Maradona.

A cewar Osimhen, Chelsea na tattaunawa da Napoli kan cinikin tun daga ranar 1 ga watan Agusta ba tare da saka cikin tattaunawar ba.

Ɗan wasan gaba na Super Eagles ya bayyana cewa ƙunhiyar ta Blues ta yanke shawarar cin gajiyar komawarsa Al Ahli bayan da Napoli san cewa zai canja sheƙa zuwa Saudi Pro League.

Sanin cewa yana iya kasancewa cikin matsananciyar wahala bayan da yarjejeniyar Saudiya ta tafi, Osimhen ya bayyana cewa a ƙarshe Chelsea ta tuntuɓe shi ta hannun mai gidansa Hansjorg Wyss kuma ta ba shi babban albashi na yuro 130,000 a kowane mako.

Ya ƙara da cewa ungiyar na son tursasa shi ta hanyar Napoli inda ya ce yana buƙatar fam 500,000 a mako bayan ya ƙi amincewa da tayin farko na fam 130,000 a kowane mako.

Bayan haka ne ɗan wasan da ya fi yin fice a Afirka ya samu aro na tsawon kakar wasa zuwa Galatasaray a gasar Super Lig ta Turkiyya.

Zakarun na Turkiyya sun cimma yarjejeniya da Napoli domin biyan gaba ɗayan albashin Osimhen a duk tsawon lokacin da ya ke a matsayim ɗan wasan aro.

By ukarofi