Kano: An gurfanar da mijin da ake zargi da kashe matarsa da banka wa ɗakinsu wuta

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar Kotun Jihar Kano ta gurfanar da wani mutum mai suna Ali Sulaiman Adam, mazaunin unguwar Gadon ƙaya, bisa zargin kashe matarsa, Maryam Nababa Badamasi, a wani lamari da ya ja hankalin al’umma a jihar.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ta 15, inda gwamnatin jihar ta shigar da tuhume-tuhume guda biyu a kansa da suka haɗa da kisan kai da kuma ƙona dukiya da gangan.

A cewar masu gabatar da ƙara, ana zargin Ali Sulaiman Adam da kashe matarsa sannan ya banka wa ɗakin da lamarin ya faru wuta domin ɓoye alamun aikata laifin.

A lokacin zaman kotun, an karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa, amma ya musanta dukkanin zarge-zargen.

Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Lamido Abba Soronɗinki, ya roƙi kotun da ta ba da damar ɗage shari’ar domin gwamnati ta shirya tare da gabatar da shaidunta a gaban kotu.

Sai dai lauyan wanda ake tuhuma, Barista A.A. Dabo, ya roƙi kotun da ta ci gaba da mutunta belin da Babbar Kotun Jihar Kano da ke Gezawa ta bai wa wanda yake karewa tun farko.

Kotun ba ta amince da wannan buƙata nan take ba, lamarin da ya sa lauyan ya nemi izinin sake shigar da sabon ƙorafin neman beli.

Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji na Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ta 15 ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Yulin 2026, lokacin da kotun za ta saurari sabon buƙatar neman belin da aka gabatar.

Shari’ar na ci gaba da jan hankalin jama’a a Kano yayin da ake sa ran kotun za ta fara cikakken sauraron ƙarar a zaman da ke tafe.

By ukarofi

Leave a Reply