Kano: Gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Kurmi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rahotanni daga jihar Kano sun bayyana cewa, a tsakar daren ranar Asabar ne gobara ta kama wani sashi na kasuwar Kurmi da ke yankin Jakara ƴan Jagwal a jihar.

Ƴan sanda a babban ofishin Jakara sun sanar da Hukumar Kashe Gobara ta jihar batun da misalin ƙarfe 1:35 na dare, inda cikin gaggawa ta tura jami’ai wajen da abin ya faru domin kai ɗauki.

A yayin isa wajen ne suka samu shaguna shida sun ƙone ƙurmus, yayin da wasu biyar kuma suka fara ci da wuta.

Daga nan ne suka samu nasarar kashe wutar da kuma ceto miliyoyin dukiyoyi daga salwanta.

A sanarwar da Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar, ya ce an samu kashe gobarar ne a yayin da ta ke ƙoƙarin lanƙwame wasu yankuna tare da tseratar da shaguna da dama.

Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya ce sun samu wani rahoton gobarar a kasuwar a ranar 15 ga watan Afrilu.

Ya kuma ce, za su yi bincike game da musabbabin faruwar gobara biyun da kuma ƙoƙarin ƙaurace wa aukuwar irin haka a nan gaba.

By Babaji