‘Yan bindiga a Kano sun kashe mutum biyu da garkuwa da ɗan attajiri a kasuwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

An harbe wasu mutane biyu tare da yin garkuwa da wani a kasuwar ƙauyen Faruruwa dake Ƙaramar Hukumar Shanono a Jihar Kano.

Wani shaida daga ƙauyen ya ce maharan sun farmaki kasuwar ne a lokacin da mutane ke ƙoƙarin rufe shagunansu bayan kammala cin kasuwa.

Ya ce, an kai harin ne da nufin samun wani hamshaƙin ɗan kasuwa, wanda an taɓa sace matarsa a baya, kana daga bisani aka sako ta bayan biyan kuɗin fansa.

Ya kuma ce, maharan kai-tsaye suka nufi shagon attajirin tare da yin garkuwa da ɗansa kasancewar ba su same shi ba.

Ƙauyen Faruruwa ya na wani yanki ne dake iyaka da Jihar Katsina, lamarin da ya sa ake ganin ƴan bindigar daga nan suka taho domin kai farmakin.

By Babaji