Yadda ake yaɗa rahotanni masu ruɗarwa game da Shettima – Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ƴan kwanakin nan ne aka kitsa makirci da batutuwan ƙarairayi akan Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ofishinsa.

An tsirar da rahotonnin ƙarya ne akansa da nufin haddasa ruɗani gami da rashin jituwa a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja.

A wata takarda da babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha ya fitar, ya yi bayani akan wani batu da ke nuna cewa an hana Shettima shiga Fadar, wanda a zahiri batu ne na ƙarya.

Ya ce, wasu rahotonni daga kafafen sadarwa sun yaɗa cewa jami’an tsaro sun hana shi shiga Fadar, wanda ƙirƙira ce daga wasu da ke ƙoƙarin ruɗar da tunanin waɗanda ba su san abinda ke faruwa a gwamnati ba.

A farkon makon da ya gabata ne Fadar ta yi watsi da wani batun bogi makamancin wannan da ya shafi ɗaukar nauyin yaɗa hotunan Shugaba Bola Tinubu na neman zaɓe.

Nkwocha ya ce, Shettima ya duƙufa ne wajen gudanar da ayyukansa da tallafa wa Shugaba Tinubu wajen cimma kayawawan manufofinsa na inganta ƙasa da al’ummarta.

Ya kuma yaba wa ƴan Nijeriya bisa kyawawan fatansu ga gwamantin Shugaba Tinubu da yaƙar yaɗa labaran ƙarya acikin al’umma.

Kazalika, ya yi kira ga al’umma da ta ƙaurace wa ɗaukar labaran bogi da wasu kafafen labarai ke fitarwa da nufin ruɗar da su.

By Babaji