
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ƙoƙarinta na inganta lamuran tsaro a jihohin Nijeriya bisa umarnin Sufeto Janar na rundunar ‘yan sanda Olatunji Disu, reshenta na Kano ya gudanar da zaman na musamman a yankin Ƙaramar Hukumar Dala domin warware matsalolin daba da suka addabi sassan jihar.
An gudanar da zaman ne a ranar Talata, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori domin samar da hanyoyin magance matsalolin daba da sauran miyagun ayyuka da suka addabi jama’a a Dala da kewayenta.
Da take jawabi a taron, Kodinetan Mata ta Ƙasa ta kwamitin hulɗa da jama’a na ‘yan sanda (PCRC) kuma mai ba gwamna shawara akan harkokin ‘yan sanda ga jama’a, Barista Maimuna Umar Sheriff, ta ce akwai buƙatar jama’a su karɓi lamuran gudanar da tsaro a yankunansu.
Ta ce, mazauna sune suka san ababen da ke faruwa a cikin unguwanninsu da waɗanda ke da hannun a aikata miyagun laifuka, tana mai kira ga al’umma da kada su bari ire-iren haka su cigaba da zama barazana ga rayuka da dukiyoyinsu.
Shi ma Shugaban ƙaramar hukumar, Hon Surajo Ibrahim Imam ya yaba wa kwamishinan ‘yan sandan bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da tsaro a jihar da kuma damawa da al’umma domin samun cikakken goyon baya a lamuran tsaro.
Kwamishinan ya kuma kirayi al’umma da su cigaba da kasancewa masu sanya ido game da ababen da ke faruwa a yankunansu tare da ruwaito dukkan wani abin zargi ga jami’an rundunar.







