Ba a magance tsaro cikin dare ɗaya – Dikko Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Tsaro ba a magance shi cikin dare ɗaya, yana buƙatar fahimta mai zurfi da tsarin haɗin gwiwa: Inji-Gwamna Raɗɗa

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa a yanzu Jihar Katsina ta zama wani abin koyi na zahiri wajen nazarin yadda ake haɗa kai da al’umma a harkokin tsaro, yana mai cewa zaɓen jihar domin wannan rangadin karatu ba haka kawai aka yi shi ba.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin mahalarta jwasa-kwasai na manyan hafsoshi na 48 daga Kwalejin Horas da Hafsoshin Sojoji ta Rundunonin Najeriya da ke Jaji (Armed Forces Command and Staff College), waɗanda suka ziyarci jihar domin rangadin karatu.

Tawagar ta ƙunshi mutane 91, ciki har da malamai da ma’aikatan gudanarwa, ɗaliban hafsoshin soja daga rundunar ƙasa, ruwa da na sama, da kuma mahalarta daga ƙasashen waje kamar Gambiya, Côte d’Ivoire da Laberiya.

Sun zo Katsina ne a matsayin wani ɓangare na rangadin nazarin muhalli mai taken: “Ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma domin inganta tsaro da wadata ta ƙasa.” Ziyarar ta bai wa gwamnatin jihar damar nuna hanyoyin aiki na zahiri wajen magance rashin tsaro da kuma bunƙasa ci gaba.

“Tsaro ba abu ba ne da za a magance cikin dare ɗaya. Yana buƙatar fahimta mai zurfi da kuma tsarin aiki na haɗin gwiwa. Muna da yakinin cewa wannan nazari da kuke yi zai taimaka wajen samar da mafita mai amfani ga ƙasa,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Gwamnan ya bayyana dabarun gwamnatinsa na tsaro da suka dogara da al’umma, tare da jaddada ƙudirin sa na ƙarfafa tsaro ta hanyar haɗa kan jama’a.

Ya bayyana taken rangadin a matsayin wanda ya dace da halin tsaron da Najeriya ke ciki a yanzu, yana mai cewa dole ne mafita mai ɗorewa ta haɗa da al’umma.

“Irin wannan nazari shi ne abin da ƙasa ke buƙata a wannan lokaci. Yana taimaka mana fahimtar rawar da al’umma za su taka wajen ƙarfafa tsarin tsaronmu a matakin jiha da na ƙasa baki ɗaya,” in ji shi.

Ya kuma bayyana cewa irin waɗannan rangadin nazari na da muhimmanci wajen inganta ilimin hafsoshin soja da samar da bincike mai amfani wanda zai iya tasiri a manufofin gwamnati ba kawai a Najeriya ba har ma a nahiyar Afirka.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa kafin zuwan gwamnatinsa, Jihar Katsina ta fuskanci manyan ƙalubalen tsaro, inda wasu ƙananan hukumomi suka kasance cikin barazana.

Ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa jami’an tsaro na gargajiya kaɗai ba su isa su magance matsalar ba.

“Mun fahimci cewa yawan sojoji, ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya bai kai abin da ake buƙata ba domin kare ƙasa yadda ya kamata. Wannan ne ya sa muka rungumi tsarin tsaro da al’umma ke jagoranta,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yawancin hare-haren tsaro na faruwa ne a yankunan karkara masu nisa, inda ɗaukar mataki kan ɗauki lokaci mai tsawo, don haka akwai buƙatar samar da matakin kariya na farko daga cikin al’umma tare da bayanan sirri na cikin gida.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa rashin tsaro a Katsina ya fi kasancewa na aikata laifuka kamar satar shanu da garkuwa da mutane, ba wai na akida ba, don haka haɗin gwiwar al’umma na da matuƙar muhimmanci.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin waɗannan laifuka suna samun goyon baya daga cikin al’umma, wanda ya sa ake buƙatar haɗin kai a matakin ƙasa.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana kafa rundunar Katsina Community Watch Corps a matsayin wani babban mataki, inda ya ce an ɗauki mambobinta ta hanyar tsari, an horas da su ta hannun sojoji da ‘yan sanda, sannan aka tura su domin taimakawa jami’an tsaro na hukuma.

By ukarofi