
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Nasarawa, ta tabbatar da sako ɗaliban Jami’ar Nasarawa da ke Keffi da aka sace a reshenta na Gudi, yayin da aka kama mutane biyu da ake zargi da hannu a ciki.
Masu garkuwar sun kutsa rukunin gidajen ɗalibai ne da ke Anguwar Ninzo a garin Gudi da ke Ƙaramar Hukumar Akwanga, inda suka sace mutane bakwai da suka haɗa da ɗaliban injiniyanci na jami’ar guda shida da wani baƙo tare da tafiya da su wani wajen da ba a sani ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar al’amarin a Lafiya, ranar Talata cikin wata sanarwa.
Ya ce, a yanzu haka ɗaliban suna karɓar magani da dukkan agajin da ya dace da halin da suke ciki yayin da aka damƙa su ga iyalansu.
SP Nansel bayyana cewa, jami’ansu sun yi nasarar kama mutane biyu da ake zargi da hannu a garkuwar bayan samun wani bayani na sirri, lamarin da ya sa suka ƙaddamar da samame akansu.
Ya ƙara da cewa mutane biyun sune Abdullahi Yeyi Haro, wanda shi ne ake zargin shugaban tawagar da kuma Basiru Abdullahi, waɗanda dukkan su ‘yan Gudi ne.
Kazalika, rundunar ta yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da suka yi wajen nuna ƙwarewar aiki da ƙoƙarin tabbatar da bada kariya ga mazauna a sassan jihar.
Haka kuma, ta ce ana cigaba da gudanar da bincike inda ake fatan kama dukkan wanda aka samu da hannu a ciki domin gurfanar da su don su fuskanci hukuncin doka, tana mai kira ga al’umma da su cigaba da ba jami’an haɗin kai wajen daƙile miyagun laifuka a yankunansu.
