Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Zaɓe ta Kano, KANSIEC ta damƙa wa sabbin ciyamomin ƙananan hukumomi 44 da ke jihar shaidar kama aiki bayan kwana ɗaya da kammala zaɓe.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Malumfashi shi ya jagoranci taron bada shaidar a yayin tabbatar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomin, ya na mai kira a gare su tare da kansiloli da su cika ayyukansu yadda ake buƙata don amfanin yankunansu.
Rahotonni sun bayyana cewa, nan ba da jimawa ba Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rantsar da su a gidan gwamnatin jihar.
Jam’iyyar NNPP ce ta lashe kujerun duka ciyamomi 44 na jihar da kansiloli 484 gundumomin faɗin jihar.
Jam’iyyun da suka fafata a zaɓukan sun haɗa da NNPP, AA, AAC, Accord, ADC da kuma APM inda NNPP wadda ke mulki a jihar ce kaɗai ta yi nasara a zaɓen.
Da farko dai, Babbar Kotun jihar ta rushe cantatar shugaban na KANSIEC daga matsayinsa a hukumar sakamakon zargin sa da alaƙa da wata jami’yya wanda hakan ya saɓa wa dokar muƙamin nasa.
Kwana ɗaya kafin zaɓen ne, Gwamna Abba ya ce za a gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara shi, wanda kuma haka aka yi.