
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Haɗaka ta bada Gurbin Karatu ga ɗalibai, JAMB ta shawarci ƙungiyar ɗaliban makarantun Polytechnics (NAPS), cewa ɗaliban HND da ba a tantace su ba ga tafiya hidimar ƙasa ta NYSC, su kai kokensu ga hukumomin da suka dace.
A lokacin da ya ke ganawa da shugaban NAPS a hedikwatar hukumar da ke Abuja, Rijistiran JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa, kamar yadda JAMB ba ita ke da alhakin bai wa ɗaliban HND gurbin karatu ba, haka kuma ba ita ce mai tantance su ba.
Farfesan ya yi mamakin yadda ƙungiyar ta tunkare su da maganar duk da cewa ba ita ke da alhakin hakan ba, ya na mai cewa akwai buƙatar a fahimci inda ya kamata a kai kukan hakan kafin a tuntuɓe su.
Ya ƙara da cewa, ayyukan JAMB sun haɗa da shirya jarrabawa ga ɗalibai masu neman gurbin shiga jami’a, ND da kuma NCE, amma banda masu HND.
Daga ƙarshe, NAPS ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Comarede Ridwan Opeyemi sun bayyana gamsuwarsu game da bayanin Farfesan da kuma ƙoƙarin tunkarar hukumar da ta dace wajen warware matsalar tantancewar.
