Ayyukan ƴan ta’adda na da alaƙa da watsi da aka yi da su – Sheikh Gumi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya ƙaryata iƙirarin da ake yi na cewa ƴan siyasa ke ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci a Arewacin Nijeriya.

Gumi wanda sananne ne akan sharhin ayyukan ta’addanci da ke cigaba da ta’azzara a shiyyar, ya ce tashin-tashinar yankin ta na da alaƙa da watsi da aka yi da waɗansu mutane na tsawon lokaci a madadin siyasantar da al’amarin.

Sanannen abu ne a ƴan shekarun nan, yankin Arewa-maso-Gabashin Nijeriya na fama da matsalolin ta’addancin kashe-kashe da yin garkuwa da mutane ciki har da kisan Sarkin Gobir na jihar Sakkwato da aka yi a kwanan nan.

Yayin da gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ya zargi ƴan siyasa da ɗaukar nauyin tashin-tashina, Gumi ya yi watsi da hakan a wata hira da jaridar PUNCH.

Malamin ya ce, “wannan zargi ne mara kan-gado. Babu wani ɗan siyasa da ke ɗaukar nauyin mutanen nan. Dukan mu abin ya shafe mu. Ɓangaren adawa ba sa goyon bayan haka. Wannan bayyana damuwa ce ta wasu mutane da aka ƙyale su na ɗaruruwan shekaru babu ilimi.”

Ya bayyana cewa, abin da ya sa lamarin ke ƙara ta’azzara shi ne fahimtar tauye haƙƙi da waɗansu al’umma ke ganin ake musu ta hanyar mayar da su saniyar ware musamman makiyaya.

Ya ƙara da cewa, yanzu mutanen su na iya shiga yanar gizo kuma su na ganin yadda ake tauye musu haƙƙi wanda akan haka su ke naman mayar da martani, don haka ya ce wannan ba shiri ne na kowaye ba.

Daga ƙarshe, Malamin ya yi kira ga gwamnati da ta dubi ainihin dalilan da suke sabbaba hakan tare da ɗaukar matakan magance su don daƙile ayyukan ta’addanci a ƙasar.

By Babaji