
Daga BELLO A. BABAJI
Darakta-Janar na Majalisar Shari’a ta Ƙasa, Aliyu Abubakar, ya tabbatar ta ƙoƙarin da su ke yi wajen bada wakilci na Shari’a ga masu zanga-zangar tsadar rayuwa da aka tsare ba tare da wani ɗauki a hukumance ba.
Cikin wata hira da ƴan jarida, Abubakar ya ce kawo yanzu majalisar ba ta tuntuɓi wasu mutane ko wata kotu ba game da wakiltar ɗaya daga cikin waɗanda aka tsaren yayin da ake cigaba da gudanar da shari’ar.
A ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ne aka gudanar da zanga-zangar kan halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki inda rahotonni suka bayyana cewa aƙalla mutane 1,200 aka kama kan zargin su da cin amanar ƙasa da wasu laifukan ta’addanci.
Ya ce, akwai buƙatar a samu wakilci na doka ga masu zanga-zangar domin ba su kariya a yayin gudanar da shari’ar inda a rashin haka ne, sai kotu ta wakilta lauya don ya tsaya a madadin mai kare su.
Abubakar ya ce, majalisar a shirye ta ke ta bai wa waɗanda aka tsare kariya matuƙar babu wanda zai ƙare su a yayin da aka gurfanar da su a gaban ƙuliya.
