Zamfara: Bello Turji ya rage harajin da ya sanya wa Moriki zuwa miliyan N30

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shahararren ɗan jaridar nan, Bulama Bukarti ya wallafa a shafinsa na X cewa an ƙulla yarjejeniya tsakanin sanannen shugaban ƴan ta’addar nan, Bello Turji da al’ummar yankin Moriki da ke jihar Zamfara.

An shirya yarjejeniyar ce wadda ta ƙunshi kuɗi da za a biya kan dabbobin Turji da aka kashe.

Acikin jawabin, Turji ya buƙaci Naira miliyan 50 ne da farko wanda daga baya ya rage adadin kuɗin zuwan miliyan N30.

A ƙarƙashin haka, kowane magidanci zai biya N10,000 yayin da samarin da basu da aure za su biya Naira dubu biyu-biyu.

Ya ce, mutanen Moriki ne suka roƙi Bello Turji ya rage musu adadin kuɗin zuwa miliyan N30 inda ya amince tare da saka musu wa’adin ranar Laraba a matsayin lokacin da za ba shi kuɗin.

Ya ƙara da cewa, kuɗin ya na matsayin biya ne ga kisan dabbobin Turji da sabon kwamandan rundunar sojojin Moriki ya yi.

Duk da cewa Kwamandan ya yi kira ga mutanen akan kar su biya kuɗin tare da yin alƙawarin ba zai sake kashe dabbobin Turji ba, haka ya bar mutanen cikin kokwanto kan abin da ka iya biyowa baya matuƙar suka amince da shawarar tasa.

Sun ji tsoron matuƙar ba su amsa buƙatar Turji ba, to za su iya fuskantar fitinar da babu wanda zai tsaya musu akai daga ɗan ta’addar.

A halin yanzu dai akwai kusan ƙananan ƴan siyasa 15 da ke tsare a hannun Turji waɗanda aka yi garkuwa da su a Moriki duk da cewa akwai jami’an sojoji a yankin.

By Babaji