Kara jari: Manyan bankuna 30 sun cika sabbin sharuɗɗan CBN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar cewa, manyan bankuna 30 a faɗin ƙasar sun riga sun samu damar cika sabbin sharuɗɗan mafi ƙarancin jari da bankin ya gindaya a cikin shirin sake ƙarfafa jarin bankuna.

Sanarwar ta fito ne a safiyar ranar Asabar ta bakin Muƙaddashin Daraktar Sashen Hulɗa da Jama’a na bankin, Hajiya Hakama Sidi Ali.

Ta bayyana cewa zuwa ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2026, shirin ƙarfafa jarin bankuna na tafiya yadda ya kamata, inda bankuna 30 suka riga suka cika sabon mafi ƙarancin jari da aka tanada bisa lasisin da kowanne banki ke da shi.

A cewar bankin, gaba ɗaya bankuna 33 sun samu ƙarin jari ta hanyoyi daban-daban, ciki har da sayar da hannayen jari ga tsofaffin masu hannun jari, fitar da hannayen jari ga jama’a a kasuwa (IPO), da kuma sayar da hannayen jari ga masu zuba jari na musamman.

Sai dai bankin ya ce har yanzu ana duba takardun wasu bankunan domin tabbatar da cikakken bin ƙa’idojin shirin kafin a sanar da sakamakon ƙarshe.

Babban Bankin Nijeriya ya ƙaddamar da wannan shiri na sake ƙarfafa jarin bankuna a shekarar 2024, inda ya gindaya sabbin ƙa’idoji ga bankuna daban-daban.

A sabon tsarin, an buƙaci bankunan kasuwanci masu lasisin aiki a ƙasashen waje su mallaki jarin aƙalla naira biliyan 500, yayin da bankunan da ke aiki a matakin ƙasa za su mallaki naira biliyan 200. Bankunan da ke aiki a matakin yanki kuwa an gindaya musu mafi ƙarancin jari na naira biliyan 50.

Haka kuma, bankunan da ke gudanar da harkokin kuɗi bisa tsarin Musulunci a matakin ƙasa an buƙaci su mallaki jari na naira biliyan 20, yayin da irin waɗanda ke aiki a matakin yanki za su ƙara jarinsu zuwa naira biliyan 10.

Babban bankin ya kuma sanya ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2026 a matsayin ranar ƙarshe da dukkan bankuna za su kammala cika waɗannan sharuɗɗa. Wannan mataki ya sa bankuna da dama suka shiga neman hanyoyin tara ƙarin jari domin su dace da sabon tsarin.

CBN ya bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce ƙarfafa tsarin bankuna a Nijeriya domin su kasance masu ƙarfi, dawwamammu, kuma masu iya tallafa wa ci gaban tattalin arzikin ƙasa a nan gaba.

Tun bayan ƙaddamar da wannan tsari, bankuna da dama sun fara ɗaukar matakai domin ƙara ƙarfin jarinsu bisa sabbin ƙa’idojin da aka gindaya.

Har ila yau, Babban Bankin Nijeriya ya jaddada cewa tsarin bankunan ƙasar yana nan daram kuma cikin ƙoshin lafiya. Ya kuma tabbatar da cewa shirin sake ƙarfafa jarin bankuna na tafiya yadda ya kamata, kuma zai ƙara ƙarfafa bankunan domin su iya tallafa wa iyalai, ‘yan kasuwa, da kuma bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Bankin ya kuma ba jama’a tabbacin cewa zai ci gaba da sa ido sosai kan bankunan da ke ƙarƙashinsa domin tabbatar da cewa sun bi dukkan ƙa’idojin da suka shafi kuɗi da jarin da aka gindaya.

By ukarofi