Kasafin 2025: INEC ta nemi a ba ta biliyan N126 madadin N40bn da aka ware ma ta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ƙi amincewa da Naira biliyan 40 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata daga Kasafin shekarar 2025 inda ta nemi majalisa da ta amince a ba ta biliyan N126 ta hannun kwamitin INEC da harkokin zaɓe.

A ranar Juma’a ne Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar da buƙatar hakan ga kwamitin a lokacin da ya ke kare kasafin.

Farfesan ya bayyana cewa harkokin zaɓe yanzu a Nijeriya sun ƙara nauyi wajen gudanar da su, ya na mai cewa a saboda haka ne suke buƙatar isassun kuɗaɗe.

Ya ce aƙalla su na buƙatar biliyan N126 waɗanda kuma sun tsara yadda za a sarrafa su daki-daki idan an ba su.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa N40bn ba za ta wakilci ɗaya bisa uku na aikin da za su yi ba don haka ya ke kira ga kwamitin da ya gabatar da buƙatarsu waɗanda suke a hukumance.

Ya ce la’akari da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi a Nijeriya, zaɓukan mazaɓu 21 da na gwamnan Anambara da za a gudanar a wannan shekarar kaɗai za su lanƙwame N40bn.

A lokacin da ta ke magana, Sanatar Abuja, Ireti Kingibe ta nuna buƙatar samar da adadin kuɗaɗen da hukumar ta nemi a ba ta la’akari da yanayin da ta ke fuskanta.

Daga nan ne kwamitin tare da shugaban hukumar da Kwamishinonin Tarayya suka shiga bayan fage domin tattauna yadda za a samo kuɗin ga hukumar.

By ukarofi