
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da Gwamnatin Tarayya take cigaba da shirye-shiryen gabatar da Kasafin shekarar 2026, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa mambobin Majalisar Wakilai wasiƙar neman su amince da shirinsa na aiwatar da hukunce-hukuncen karɓo rance na Dokar Kasafi ta 2026, wanda adadinsa ya kai Naira tiriliyan 10.8. Shugaban ya ce, shirin aro kuɗin yana da nufin amfani da kuɗaɗen wajen aiwatar muhimman ayyukan raya ƙasa da aka sanya cikin Dokar Kasafi don ƙarfafa wa ribar tattali da aka samu a ƙarƙashin gwamnatinsa.
A ‘yan kwanakin nan ne dai gwamnatin Tinubu take shan suka kan cigaba da karɓo rancen kuɗaɗe daga ƙasashen waje, inda masu sharhi ke ganin hakan ka iya jefa ƙasar a matsananci halin bashi a madadin ceto ta daga ƙalubalen kuɗaɗen da take fuskanta.
Saidai, gwamnatin ta kare matakin nata, inda ta ce Nijeriya na buƙatar zuba jari na tsawon lokaci domin cimma muradinta na zama mai tattalin Dala tiriliyan 1 zuwa shekarar 2030. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta gargaɗi buƙatar gwamnatin ta neman amincewar Majalisar Dokokin Ƙasa ga ciyo bashin Dala biliyan 20.5 da Yuro biliyan 1.45, duk da iƙirarin cewa kuɗin shigar gwamnatin ya ƙaru a sakamakon cire tallafin fetur.
A wata sanarwa da aka yi wa laƙabi da ‘From Reforms to Delivery: Our Infrastructure Investment and Growth Strategy’, wato “Daga Gyare-gyare zuwa Isarwa: Zuba Jarinmu a Ababen More Rayuwa da Dabarun Bunƙasa”, Tinubu ya ce ya dace a riƙa mayar da hankali kan abin da ake yi da kuɗaɗe idan an karɓo su, ba tambayar adadinsu ba.
Ya zayyano muhimman ayyukan ababen more rayuwa da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin nasa kama babban titin Sakkwato zuwa Badagry, babban titin yankunan sahara da layin dogo a Arewacin Nijeriya, ci-gaba a rumbun lantarki na ƙasa da bunƙasa muhimman tashoshin ruwan Legas da dai sauransu da gwamnatin ke neman ƙarfafa wa ta fuskantar kuɗi da rancen, kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana cewa, ayyukan tare da zuba jari a fannin kiwon lafiya, ilimi, da horarwa kan sana’o’i, za su taimaka wajen sadar da ribar tattali, rage tsadar sufurin kayayyaki, tallafa wa noma da masana’antu da kuma janyo ra’ayoyin masu zuba jari, yana mai cewa babbar titin Legas zuwa Badagry kaɗai ka iya samar da ayyuka 100,000 da ƙarin wasu ayyuka 150,000 a harkar jigilar kayayyaki, kayan gini da dangoginsu.
