Kebbi: MSSN ta yi jimamin rashin shugabanta na Yauri da ƴan bindiga suka halaka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hedikwatar Ɗalibai Musulmi ta Ƙasa (MSSN) ta nuna kaɗuwarta game da rashin Shugabanta na yankin Yauri a Jihar Kebbi, Ustaz Alqasim Usman Ibrahim, wanda ƴan bindiga suka halaka a makom da ya gabata.

A cewar MSSN, an yi garkuwa da mamacin ne a gonarsa a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2025, inda bayan kwana guda da faruwar haka aka tabbatar da rasuwarsa.

A wata sanarwa da Sakataren hulɗa da jama’arta, Moshood Abiola Olatunbi ya fitar, MSSN ta bayyana rashin a matsayin abin takaici da ke ƙarfafa ta’azzarar matsalar tsaro a yankunan Musulmi da ke sassan Nijeriya.

Ƙungiyar ta kuma ce, marigayin ya kasance jajirtaccen shugaba abin koyi bisa hidimarsa ga addini Islama, wanda hakan ke taimakawa wajen inganta rayukan matasan Musulmi.

Kazalika, ta yi addu’ar Allah ya jiƙan sa ya gafara masa kurakuransa tare da karɓar kyawawan ayyukansa gami da sanya shi a Aljannar Firdausi.

By Babaji