Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi.
Malamai guda 100 mabiya ɗariqatul tijjaniyya da masu aƙiidar Izala daga ulama na Jihar Kebbi suka hallara a ɗakin taron masaukin shugaban ƙasa dake Birnin Kebbi, ranar Jumu’a da ta wuce, suka nuna yabo ga Allah na cika shekara uku akan karagar mulkin na gwamnatin Kwamred, Dakta Nasir Idris, a matsayin gwamnar Jihar Kebbi mai cikakken iko.
Gwamnatin Jiharce ta kira taron domin gudanar da addu’oi masu zurfi, na samun nasarar zaɓen 2027, da kuma zaman lafiya mai ɗorewa a Kebbi da kuma ƙasa baki ɗaya.
Da yake share fage, babban sakatare a ma’aikatar kula da harkokin addini ta Jihar Kebbi, Muhammad A. Bala, yace an gayyato malaman ne, domin yima shugabanni da sauran al’ummar wannan ƙasaitacciyar ƙasar mu, addu’oi na samun rahamar Allah.
“Gwamnarmu, mutum ne mai Taqwa, gwamnatinmu, gwamnatin addu’a ce, wadda aka daɓbaƙa akan addu’a, saboda addu’a itace ginshiƙin samun nasarar rayuwar dan-Adam a kowane fanni”,
Dakta Nazifi Abubakar Nyass ne na ɗariqatul Tijjaniyya, ya fara hawan mimbari, wurin addu’oin, ya roƙi Allah ya kawo ƙarshen kalubale na rashin tsaro da ake fama da shi a cikin ƙasar mu; sannan kuma ya kare al’ummarmu daga sharrin ‘yan bindiga da masu kashe-kashen rayuka.
Sheikh Aliyu Ladda Bunza, Shugaban Izala, shi kuma, yabo ya yi ma Gwamna Nasir Idris dangane da yadda yake kulawa da harkokin addini, musamman ƙirƙiro da ma’aikatar kula da harkokin addini da yayi jim-kaɗan bayan ya zama gwamnar Jihar Kebbi.
Sauran malaman da suka hau mimbari sune, Farfesa Muhammad Abubakar Wali, da Sheikh Na-Taraba Yauri, da Sheikh Usman Na-ayi Jega, da kuma Asheikh Isa Ibrahim Wala, a inda sukayi addu’oin, Allah ya ƙara sanya ma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da Gwamna Nasir Idris, basira da lafiya da kariya-daga duk wani sharri, wurin jagorancin da suke ma al’umma.
Sun roƙi Allah ya basu cikakkiyar nasara a babban zaɓen ƙasa da za’ayi a Najeriya a shekarar 2027.
A sharhin da yayi, Gwamna Nasir Idris, ya jinjina ma malaman dangane da goyon bayan da suke bai wa gwamnatin-APC mai mulki a yanzu, a matakin gwamnatin tarayya da na jiha.
“Muna masu matuƙar jin-daɗi ganin yadda kuke nuna ƙauna da goyon baya garemu da kuma gwamnatinmu a ko yaushe”,
“Gwamnatinmu ta sanya addini a matsayin mizani, muna masu yarda da hukubcin Allah da kuma Sunnah ta Manzon Allah SAW, sannan kuma, mun yi imanin cewar addu’a, na da tasiri, ita ke kaiwa ga nasara wurin nemar biyan buƙata”,
“Wannan gwamnati mai-ci yanzu, za ta cigaba da daraja harkokin addini da kuma mutunta malamai”, Gwamna Nasir Idris ya bada tabbaci.
Qadi Muhammad Sani Randali, ya wakilci babban-Qadi (Alkalin- Alkalai) na Jihar Kebbi, Khalifah Ahmad Usman Mukhtar, a zaman taron addu’oin da aka gudanar.
