Kenya: An yanke wa ‘yar wasan tsere hukuncin shekara guda saboda amfani da maganin ƙara kuzari

Daga FATUHU MUSTAPHA

Wata kotun ƙasar Kenya ta yanke wa ‘yar wasan tseren asar, Florence Jepkosgei, hukuncin yi wa al’umma hidima na tsawon shekara guda bayan da ta kama ta da laifin gabatar da takardun bogi na ƙoƙarin kare kanta daga laifin yin amfani da ƙwayoyin ƙara kuzari, in ji Ƙungiyar Yaƙi da Amfani da Abubuwan Ƙara Kuazara ga ‘Yanwasa ta Kenya (ADAK).

Da wannan, Florence ta zama ‘yar tseren Kenya ta farko da aka taɓa yanke wa hukuncin manyan laifuka a kotu.

An shafe shekaru ana gudanar da bincike kan wannan batu kafin a kai ga yanke hukunci a wannan lokaci.

Florence, ‘yar shekara 36, an dakatar da ita tsawon shekara biyu daga barin yin wasa a 2017 bisa laifin shan ƙwayoyin ƙara kuzari.

An kama Florence da laifin gabatar da takardun asibiti na bogi a lokacin da take ƙoƙarin kare kanta a kotun sauraren ƙararrakin harkokin wasannin motsa jiki.

Sai dai, asibitin yankin Uasin Gishu ta tabbatar da cewa takardun da ‘yar wasan tseren ta gabatar na bogi ne, tare da cewa babu wani lokaci da ta zo duba lafiyarta a asibitin, kamar yadda ADAK ta bayyana.

‘Yan wasan tseren Kenya su sama da 60 aka dakatar daga barin yin wasa a tsakanin shekaru biyar da suka gabata saboda laifin shan magungunan ƙara kuazari.