Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai magana da yawun tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu, ya ce sam maigidan nasa bai yi wani abu don yi wa yunƙurin Bola Tinubu na zama Shugaban Nijeriya a 2023 zagon ƙasa ba.

Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata yayin wani taron manema labarai gabanin ƙaddamar da sabon littafin da ya rubuta a kan zamansa mai magana da yawun Buhari, wanda za a ƙaddamar ranar tara ga watan Yuli.

An dai yi zargin cewa da gangan Buhari ya jinkirta cire tallafin man fetur har zuwa ƙarshen mulkinsa a 2023 domin ya haɗa ’yan Nijeriya faɗa da Tinubu.

Kazalika, ’yan Nijeriya sun rika sukar lamirin gwamnatin Tinubu kan kawo wahalhalu da yunwa tun bayan sanar da cire tallafin man da shugaban ya yi ranar da aka rantsar da shi.

To sai dai Garba Shehu ya ƙaryata batun cewa an shirya cire tallafin ne saboda a yi wa Tinubu zagon ƙasa.

Kakakin ya ce ya cika da mamakin labarin, yana mai cewa ba yadda za a yi Buhari ya yi hakan ga ɗan jam’iyyarsa, tamkar daga wata jam’iyyar zai karɓi mulkin daga hannunsa.

Ya ce, “Da Buhari da Tinubu duk ’yan APC ne, saboda haka ban ga ta yadda za mu shirya abin da zai yi wa gwamnatinmu zagon ƙasa ba.

“Buhari mutum ne da ya tsani harkar rashawa, ya shigo gwamnati da gaskiyar shi, kuma har ya gama a haka yake. Ya yi iya bakin ƙoƙarinsa ga ’yan Nijeriya kuma tarihi ba zai manta da shi ba. shi ba mutum ba ne mai kwarmato, aiki kawai ya yi,” inji Garba Shehu.

Ya kuma ce shi a karan kansa bai yi laifi ba saboda ya kyale tsohon maigidansa kuma tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi aiki a gwamnatin Buhari.

By ukarofi