Ko kiyaye ‘yanci ya fi kare rayukan jama’a muhimmanci?

Daga AMINA XU

Abokaina, yau “duniya a zanen MINA” na mai da hankali kan haƙiƙanin ma’anar‘yanci?

Tun kafuwar ƙasar Amurka, aka gabatar da “Sanarwar samun ‘yanci”, inda aka nanata cewa, haƙƙin tabbatar da rayuka, da neman ‘yanci da kuma alheri, haƙƙin ne na daukacin Bil Adama.

Rayukan jama’a shi ne na farko, amma ‘yan siyasar Amurka suke nacewa ga tsattsauran ra’ayi game da ‘yanci, ta rashin mayar da hankali kan rayukan jama’a tun bayan ɓarkewar cutar COVID-19, inda mutane fiye da miliyan ɗaya suka mutu sakamakon annobar, ko wannan shi ne haƙiƙanin ma’anar ‘yanci?

Mai zana: Amina Xu