Wani manomi mazaunin Ibadan, Williams Famuyibo ya roƙi kotun al’ada ta Mapo Grade ‘A’ da ke Ibadan ta raba aurensa da matarsa Sola, sakamakon irin azabar da ya ke fuskanta a hannunta.
Famuyibo ya ce, ba zai iya jurewa dukan tsiya daga matarsa ba.
Ya ce, “ya mai shari’a, saboda rashin samun kwanciyar hankalin da na ke fuskanta a gida na, ina neman a raba ni da matata”.
“A gaskiya, ba ni da kwanciyar hankali domin ba ta kula da ni. Ba zan iya cigaba da jurewa duka daga Sola ba.
“Ina da ’ya’ya biyar kafin na auri Sola a shekarar 1990, amma dukkansu suna zaune da sauran ’yan uwana ne sakamakon halin kyamar Sola,” inji Famuyibo.
Duk da bayanin da aka yi mata game da sanarwar sauraron ƙarar, amma matar ba ta halarci kotun ba kuma ba ta sanya wani lauya ya wakilce ta ba a lamarin.
Shugaban kotun, S.M. Akintayo, ya umurci mai bayar da belin kotun da ya sanar da wanda ake ƙara ranar da za a ɗage sauraron ƙarar.
Akintayo ta ɗage sauraron ƙarar har sai ranar 26 ga watan Mayu domin cigaba da sauraron ƙarar.