Kocin Super Falcons, Madugu da mai tsaron gida Nnadozie sun shiga sahun ƴan takarar Ballon d’Or

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai tsaron ragar tawagar Super Falcons, Chiamaka Nnadozie da Koci Justine Madugu sun shiga sahun ƴan takarar kyautar Ballon d’Or ta 2025.

An sanya sunan Chiamaka ne cikin ƴan wasa mata da ka iya lashe kyautar Yachine yayin da aka zaɓi Madugu a jerin waɗanda ka iya lashe na gwarzon mai horaswa na shekarar.

Mai tsaron gidan ta Brighton tana ɗaya daga cikin yan wasa biyar da aka zabe su a rukunin.

Sun haɗa da Ann-Katrin Berger ta Jamus Germany da ƙungiyar Gotham FC, Cata Coll ta Barcelona, Hannah Hampton Ingila da Chelsea, da Daphne Van Domselaar ta Arsenal.

Tsohuwar ƴar wasan ta ƙungiyar Paris FC tana daya ƴan wasan Super Falcons da suka lashe Kofin Nahiyar Afirka na mata, wato WAFCON na 2025.

By Babaji