Korona nau’in Omicron: Birtaniya ta hana ‘yan Nijeriya shiga ƙasarta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ci gaba da ɗaukar matakan kariya da take yi, gwamnatin ƙasar Birtaniya ta sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ta ware domin ɗaukar ƙarin matakai a kan ‘yan ƙasashensu wajen shiga Birtaniyar, saboda mutane 21 da aka samu ɗauke da sabon nau’in cutar Korona omicron a Ingila, waɗanda suka je can daga Nijeriyar.

Matakin ya ƙunshi hana ‘yan Nijeriyar da ma sauran mutane daga ƙasar waɗanda ba su da fasfo na Birtaniya ko izinin zama a can zuwa.

Wata sanarwa da hukumomin Birtaniyar suka fitar ta ce daga ƙarfe huɗu na asuba agogon ƙasar wato biyar na asuba kenan agogon Nijeriya, Litinin 6 ga Disamba matakin zai fara aiki.

Matakin na nufin ‘yan Nijeriya ko mutanen da suka fito daga ƙasar waɗanda suka kai kwana goma waɗanda ba su da fasfo na Birtaniya ko takardar izinin zama a ƙasar daga ranar ba za su je ba, har sai abin da hali ya yi.

Hakan ya kuma shafi hatta waɗanda aka yi wa cikakken rigakafin Korona.

Su kuwa waɗanda suke da damar shiga ƙasar daga Nijeriyar, wato waɗanda suke da fasfo na Birtaniyar da kuma na Ireland tare da masu izinin zama, dole ne su killace kansu tsawon kwana goma a wani wuri da gwamnati ta amince da shi, da zarar sun shiga Birtaniyar.

Sannan kuma dole ya kasance masu shigar sun gabatar da shedar gwajin cutar Koronar guda biyu da aka yi musu da duk biyun suka nuna ba sa ɗauke da cutar, yayin da ake ci gaba da ɗaukar ƙarin matakan daƙile sabon nau’in cutar, Omicron.

Sai dai kuma wannan mataki kamar yadda sanarwar ta nuna bai shafi matafiya da suka yada zango domin sauyin jirgi a Nijeriyar ba, waɗanda a dalilin sauyin jirgin ne kawai aka bi da su ta can.

Haka kuma matafiya daga Nijeriyar har yanzu suna da damar bi ta filayen jirgin saman Ingila, su sauya jirgi zuwa wata ƙasar da za su je, idan dai suna da takardar izinin bi ta Birtaniyar.

Da take bayani a kan matakin, jakadiyar Birtaniya a Nijeriya Catriona Laing ta ce, matakin na wucin-gadi ne domin kare ƙaruwar mutanen da ke ɗauke da sabon nau’in cutar Korona shiga Birtaniya.

Kuma za a sake nazarin matakin bayan sati uku, wato ranar 20 ga watan Disamba kenan.

Jakadiya Laing ta ce ta san cewa wannan mataki zai shafi mutane a ƙasashen biyu sosai, musamman ma a wannan lokaci na shekara, to amma abu ne da aka yi na kan-da-garki domin kare lafiyar jama’a a Birtaniya, yayin da ake ƙoƙarin fahimtar yadda sabon nau’in cutar yake.

Ta ce suna ci gaba da aiki ƙut-da-ƙut da hukumomin Nijeriya wajen yaqi da annobar, kuma suna yabawa da aikin da Nijeriyar ke yi.

A yanzu dai yawancin mutanen da aka samu na ɗauke da sabon nau’in cutar Koronar a Birtaniya suna da alaƙa da matafiya daga Afrika ta Kudu da Nijeriya.

Kuma a makon da ya gabata mutane 21 da aka bayar da rahoton an samu ɗauke da cutar daga Nijeriya suke.