Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata kotu a Jihar Kano da ke zamanta a Gwarzo ta yanke wa wani dattijo mai shekara 85, Malam Isah, hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari bisa laifin yi wa wata ƙaramar yarinya fyaɗe.
Kotun ta bayyana cewa an aikata laifin ne a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, a ƙauyen Sauna da ke ƙaramar Hukumar Gabasawa a jihar.
Yayin yanke hukunci, Mai shari’a Aisha Mahmoud ta ce ɓangaren masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba, bayan gabatar da hujjoji masu gamsarwa a gaban kotu.
Bisa haka, kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan Shari’a na jihar kuma Babban Lauyan Jiha, Abdulkareem Kabir Maude, ya yabawa tawagar masu gabatar da ƙara bisa ƙoƙarinsu da jajircewa wajen gudanar da shari’ar.
Ya kuma jaddada ƙudurin ma’aikatar shari’a na tabbatar da an yi adalci a dukkan lamura, tare da gargaɗin cewa gwamnati ba za ta sassauta wajen hukunta masu aikata irin waɗannan laifuka ba.
