
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani tsohon jami’in rundunar ‘yan sanda ya janyo hankalin jama’a tare da nuna fargaba bayan ya yi barazanar shiga ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram saboda ƙorafe-ƙorafen da suka shafi kuɗaɗensa na fansho.
Da yake jawabi a wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, Tsoho jami’in ya yi gargaɗin ɗaukar mummunan mataki matuƙar ba a warware masa matsalar fanshonsa ba.
“Idan ba a yi komai ba game da wannan, zan koma ɗaya ɓangaren kuma na shiga Boko Haram, in riƙa taya su gyara bindigoginsu da ba su horo”, inji shi.
Ya bayyana tsarin fanshon da yake ciki a matsayin ‘bauta’, inda ya kuma nuna ɓacin ransa akan yadda aka yi watsi da shi bayan ya kwashe shekaru yana yi wa ƙasa hidima.
Waɗannan kalamai na zuwa ne yayin da tsofaffin jami’ai ke ƙara nuna rashin jin daɗinsu akan jinkirin biyan kuɗaɗensu da dokar ƙasa ta bayar da umarnin a riƙa ba su.
A watan Satumbar 2025, tsofaffin jami’an ‘yan sanda suka yi zanga-zanga a Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ke Abuja, inda suka kira tsarin fansho na CPS da salon damfara da aka ƙirƙira domin cigaba da dawwamar da su acikin talauci.
Akan haka ne Majalisar Dattawa ta amince da dokar cire ‘yan sanda daga CPS daga bisani a watan Disamba, inda Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ba su tabbacin za a amince da buƙatarsu cikin gaggawa domin shawo kan matsalolin da suke fuskanta akan al’amarin.
