Kotu da sahale wa Tukur Mamu ganin likitansa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya amince da buƙatar Tukur Mamu na ba shi damar ganin likitansa saboda rashin lafiya da ake zargin yana fama da shi.

A hukuncin da ya yanke yayin zaman kotun, Alƙali Ekwo ya ba da umarni kan a bai wa likitan Mamu damar ya duba shi ƙarƙashin kulawar tawagar hukumar DSS.

Alƙalin ya amince da bayanan lauyan Mamu, Johnson Usman, inda ya nuna ‘yancin da wanda yake karewa yake da shi na ganin likitansa don kula da lafiyarsa.

Daga bisani, Alƙalin kotun ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa 26-28 ga Fabrairun 2024.

A lokutan baya hukuma ta tsare Tukur Mamu kan zargin alaƙar da ke tsakaninsa da ‘yan ta’addan da suka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuws Kaduna hari a shekarar 2022.

‘Yan sandan ƙasa da ƙasa ne suka tsare shi a Alƙahira, ƙasar Masar, a ranar 6 ga Satumban 2022 a madadin Gwamnatin Nijeriya.

By Editor