Kotu ta ɗaure tsohon shugaban Super Lig kan naushin alƙalin wasa

Spread the love

Wata kotun Turkiyya ta ɗaure tsohon shugaban ƙungiyar Super Lig shekaru sama da uku a gidan yari saboda ya naushin alƙalin wasa.

Shugaban MKE Ankaragucu, Faruk Koca, ya naushi alƙalin wasa, Halil Umut Meler a fuska bayan busa sautin tashi na wasan Super Lig a shekara ta 2023.

Faruk Koca, ya naushi Halil Meler bayan wasan da aka tashi da ci 1-1 tsakanin Caykur Rizespor da Ankaragucu a watan Disambar 2023.

Kamar yadda rahoto ya nuna, wata kotu a Ankara ta sami Koca da laifin “cin zarafin jami’in gwamnati” kuma ta yanke masa hukuncin shekaru uku da wata bakwai a kurkuku.

Lamarin ya jawo fushin duniya baki ɗaya, inda ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Turkiyya ta dakatar da dukkanin wasannin gasar na wasu makonni.

Koca ya yi murabus daga matsayin kocin ƙungiyar bayan lamarin, wanda ya bar alƙalin wasan da rauni a gefen idonsa.

Kotun ta bayyana cewa an same shi da laifin dukan alƙalin da kuma karya dokokin da aka kafa domin hana tashin hankali a wasanni.
Abin lura a wannan tirka tirka

An ci ƙungiyar Ankaragucu tarar Euro 45,000 sannan an tilasta musu su buga wasanni guda biyar ba tare da magoya bayansu a filin ba sakamakon wannan fitina.

Wannan ya faru ne bayan da Rizespor ta ci kwallo a mintin ƙarshe na wasan. Daga bisani, Rizespor ta fita daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turkiyya a kakar wasan.

Kotu ta ƙara da cewa, ta yankewa wasu mutane uku da ake tuhuma tare da Koca kan naushin alƙalin wasan hukuncin zaman kurkuku na shekara daya zuwa biyar.

To sai dai kuma, rahotanni sun bayyana cewa Faruk Koca na shirin ɗaukaka ƙara kan wannan hukunci, inda ya ce bai gamsu da matsayar kotun ba, inji rahoton ESPN.

By ukarofi