A Talata ne sabon mai horas da ƙungiyar Manchester United Ruben Amorim ya isa Ingila don amsar ragamarta, inda ya samu tarba daga shugabannin Man United.
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce sabon mai horaswan na ta kwanaki 12 daga yanzu don shirya buga wasansa na farko a gasar Firimiya, a karawar da za suyi da Ipswich Town a ranar 24 ga wannan watan.
United dai ta naɗa Amorim a matsayin wanda zai maye gurbin Erik ten Hag da ta sallama, kuma zai ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa shekarar 2027.
Kafin amsar aikin horas da Manchester United da Ruben Amorim ya yi, ya kasance mai horas da ƙungiyar Sporting Lisbon ta ƙasar Porgugal, wacce ya taimakawa wajen lashe gasar lik ɗin ƙasar.
To sai dai zuwan Amorim mai shekaru 39, yayi awon gaba da aikin mataimakin mai horas wa ƙungiyar wanda kuma ke riƙon kwaryar aikin horas da ƙungiyar Ruud ɓan Nistelrooy tare da wasu masu horaswa uku.
Van Nistelrooy dai ya jagoranci kungiyar a wasanni 4, kuma ya samu nasara a wasanni 3 sannan ya yi kunnen doki a wasa ɗaya.
