
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ayyana matakin LPDC na dakatarwar shiga aikin shari’ar na tsawon shekara uku akan Mista Gadzama, a cewar wata sanarwa da aka aike wa jaridar PREMIUM TIMES a ranar Litinin.
Sanarwar da lauyoyin Gadzama suka fitar ta ce kotun da ayyana aiwatarwa ko tilasta hukuncin akan babban lauyan a matsayin abin da ya saɓa wa dokokin Sashe na 36(1), 36(2) da 6(6)(b) na Kundin Dokokin Nijeriya.
Sannan, sanarwar ta ce kotun ta ayyana cewa LPDC ba shi da hurumi akan al’amarin, don haka Mai Shari’a Obiora Egwatu ya haramta wa Babban Rajistiran Kotun Ƙoli ɗaukar dukkan wani matakin ladabtarwa akan Mista Gadzama akan wannan batu.
Kazalika, kotun ta kuma haramta wallafawa ko yaɗa umarnin a matsayin matakin ladabtarwa na ƙarshe akansa. Wannan hukunci ya biyo bayan da Gadzama ya ƙalubalanci matakin dakatarwar da LPDC ya yi masa na shigar harkar shari’a na tsawon shekara uku.
Rikicin ya samo asali ne daga karɓa da raba diyya mai alaƙa da shari’ar kisan gillar yankin Zaki-Biam da ya ƙunshi iƙirarin gabatarwar shari’a da ladar aikin ƙwararru masu cin karo da juna, inda aka danganta wani Mista Alashi da Gadzama kan cewa yana karɓar umarni daga wajensa. Saidai Gadzama ya musanta wannan tuhuma, inda ya ce ya samu umarni ne daga wani tsagin masu gabatar da shari’a, amma duk da haka LPDC sai da ta dakatar da shi.
