Kotu ta bada belin matar da ta yi wa Sufeton Janar da Seyi Tinubu barazana

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta yanke hukunci belin Naira miliyan 10 da sa hannun mutum ɗaya ga Olamide Thomas, wadda ta yi barazanar kisa ta soshiyal mediya ga Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun da kuma Seyi Tinubu.

A ranar Litinin, 6 ga watan Junairu ne Mai Shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin bayan nazari da ya yi game da hujjojin da masu ƙara suka shigar da na wanda ake zargi.

Allƙalin ya kuma umarci wanda zai tsaya wa mai laifin da ya gabatar da takardar shaidar biyan haraji ta shekara uku da kuma bada sauran bayanai gamsassu game da shi a matsayin sharaɗin belin.

A ranar 20 ga watan Disamba, 2024 ne aka gurfanar da matar wadda daga bisani aka tasa ƙeyarta zuwa gidan gyaran hali na Suleja bayan ta musanta aikata laifuka uku da Sufeton ya gabatar akan ta.

An kama Olamide Thomas ne bisa laifin cin mutuncin da barazanar kisa ga Seyi Tinubu da Sufeton ƴan sandan da kuma jami’in yaɗa labaran rundunar ƴan sanda, Muyiwa Adejobi.

Mai Shari’a Nwite ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu.

By ukarofi