‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu na ɗaya daga cikin yan sanda 181 da suka sami ƙarin girma a jihar.
ASP Abubakar Sadiq Aliyu da mutane 150 masu muƙamin irin nasa zuwa muƙamin DSP.
Lokacin da yake jawabi bayan ya liƙama ‘yan sandan alamun ƙarin girma, kwamishinan yan sanda CP Aliyu Abubakar Musa ya ja hankalin su da cewa wannan ƙarin nauyi ne a kansu.
“Wannan karin girma na iya janyo tura ku zuwa wasu wurin domin gudanar da aiki”inji kwamishinan.
CP Aliyu Abubakar ya kuma yi kira ga matan ‘yan sandan da aka ƙarawa girma da su guji ƙara ɗora masu wasu nauyi ganin zasu sami ƙarin albashi.
“Ku bari mazajen ku su sami damar taimaka wa ‘yan uwansu da marayu saboda suma ‘yan cikin gida ne”Kwamishinan ya ce .
