Daga USMAN KAROFI
Rundunar ‘yan Sandan vabban Blbirnin tarayya (FCT) ta tabbatar da fashewar bam da ya auku a ranar 6 ga Janairu, 2025, da misalin karfe 11:00 na safe a makarantar Islamiyya ta tsangagyar Sani Uthman da ke Kuchibuyi, Byazhin.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa fashewar ta faru ne yayin da wasu mutane uku daga Katsina suka kawo kayan fashewa zuwa makarantar, lamarin da ya kai ga mutuwar biyu daga cikinsu yayin da suke ɗauke da na’urar fashewa.
A cewar SP Adeh, bayan samun kiran gaggawa, tawagar ‘yan sanda da ke kula da fashe-fashe (EOD) tare da kwamandan wannan yankin na Kubwa sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka tsare yankin kuma suka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Mutumin da ya tsira daga cikin uku da wata ‘yar kasuwa da suka ji munanan raunuka suna karɓar magani ƙarƙashin tsaron ‘yan sanda.
Mai makarantar, Mallam Adamu Ashimu, kuma yana hannun hukuma don bincike.
Kwamishinan ‘yan sandan FCT, CP Olatunji Disu, ya yi kira ga jama’a da su kasance masu kula da muhallinsu tare da ɗaukar matakan tsaro domin kare kansu daga irin wannan lamari. Rundunar ta fitar da lambobin gaggawa da shawarwarin tsaro guda huɗu da ya kamata jama’a su bi domin rage haɗarin irin wannan lamari a nan gaba.
Matakan Tsaro Guda Hudu:
1. Kasancewa mai lura: Jama’a su kasance masu lura da abin da ke faruwa a muhallinsu tare da sanar da hukuma duk wani abu da yakamata.
2. Kada a taɓa abu da ake Zargi: Idan aka ga wani abu da ake zargin zai iya fashewa, kada a taɓa shi ko ƙoƙarin matsar da shi, a kira ‘yan sanda cikin gaggawa.
3. Adana lambobin gaggawa: A tabbata cewa an adana lambobin gaggawa domin sanar da dangi da abokai idan abu ya faru cikin sauri.
4. Kulawa a cikin al’umma: Jama’a su haɗa kai da mazauna yankinsu domin tabbatar da tsaro da gano duk wani abu ko mutum wanda ba su yarda dashi ba.
Daga ƙarshe za a iya kiran lambobin gaggawa kamar 0806 158 1938 da 0803 200 3913 idan aka samu wani abu da ya zama abin damuwa. Wannan zai taimaka wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka.
