Kotu ta bada umarnin kama tsohuwar Ministar Jin ƙai Sadiya Umar Farouk da Nura Alƙali

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin Alƙali Jude Onwuegbuzie ta bayar da izinin kama tsohuwar Ministar Jin ƙai, Sadiya Umar Farouq, da tsohon Babban Sakataren ma’aikatar, Bashir Nura Alƙali bisa zargin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe.

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, na tuhumar su da laifuka guda 21, waɗanda suka haɗa da cin amanar aiki da karkatar da kimanin dala miliyan 1.3 da kuma sama da Naira miliyan 746.5 a lokacin da suke riƙe da muƙaman.

Saidai, yayin da aka nemi su gurfanar a kotu, ba su halarta ba, inda mutum na uku mai suna Sani Nafiu Mohammed, ya bayyana. Lauyan ɓangaren gwamnati ya ce an daɗe ana ƙoƙarin gabatar da su tun Disambar 2025, amma an gaza cimma hakan.

Lauyan tsohuwar ministar ya danganta rashin zuwanta da rashin lafiya, amma kotu ta ƙi amincewa da hujjar da aka gabatar.

Daga nan ne kotu ta amince da buƙatar EFCC na bayar da sammacin kama su domin gurfanar da su a gabanta don su fuskanci hukuncin doka akan ababen da ake tuhumar su a kansu.

Bayan haka ne aka ɗage zaman sauraron ƙarar zuwa ranar 18 ga Mayu, 2026 domin fara shari’ar al’amarin.

By Babaji