
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata likita mai suna Dakta Ere Ogbachi, ta rasa ranta a Jihar Bayelsa bayan ta haifi ’yan uku, sakamakon matsalolin lafiya da suka taso mata bayan faruwar al’amarin.
Bayan haihuwar jariran a Asibitin koyarwa na jami’ar Neja-Delta da ke Okolobiri, rahotonni sun ce halin lafiyar likitar ya shiga matsanancin yanayi, wanda ya sa aka gaggauta kai ta sashin kulawa na musamman (ICU) na Babban Asibitin Tarayya da ke Yenagoa, babban birnin jihar.
Wani ɗan uwanta mai suna Meshack Sintei, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceto ranta, ta rasu da misalin ƙarfe 2:45 na daren ranar 14 ga Afrilu, 2026.
Ya ce, matakin numfashinta ya riƙa sauka sosai har ya kai sifili, kafin daga bisani ta rasu.
Marigayiyar mai shekaru 38, ƙwararriyar likitar mata da haihuwa ce, kuma ma’aikaciyar NDUTH, wadda ta bar ‘ya’ya uku, mata biyu da namiji waɗanda ke cikin koshin lafiya.
Iyalan marigayiyar sun bayyana rasuwarta a matsayin babban rashi, tare da cewa ta yi gwagwarmaya har zuwa karshen rayuwarta.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, mahukuntan asibitin ba su fitar da wata sanarwa ba a hukumance.
