Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun Babban Birnin Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar beli da tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya gabatar domin a sake shi daga tsarewar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC.
Alƙalin kotun, Mai shari’a Babangida Hassan, ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ba shi da hurumin bayar da beli, kasancewar wata kotu mai matsayi iri ɗaya ta riga ta bai wa EFCC umarnin tsare Malami domin ci gaba da bincike.
Rahotanni sun nuna cewa Malami, wanda ke daga cikin manyan jiga-jigan haɗin kan ‘yan adawa kuma mai sha’awar takarar gwamnan Jihar Kebbi, yana tsare a hannun EFCC tun daga makon jiya Litinin, bisa zargin almubazzaranci da kuɗaɗen gwamnati.
Ta hannun lauyansa, Sulaiman Hassan, SAN, Malami ya roƙi kotun da ta ba shi beli, yana mai cewa tsarewar da EFCC ke yi masa ba bisa ƙa’ida ba ce.
Sai dai lauyan EFCC, Jibrin Okutepa, SAN, ya shaida wa kotun cewa hukumar na tsare da tsohon ministan ne bisa sahihin umarnin tsarewa da wata Kotun Babban Birnin Tarayya ta bayar ƙarƙashin Mai shari’a S. C. Oriji.
Okutepa ya jaddada cewa EFCC hukuma ce mai bin doka da oda, kuma ba ta tsare mutum fiye da wa’adin da doka ta tanada ba tare da umarnin kotu ba.
A hukuncinsa, Mai shari’a Hassan ya ambaci Sashe na 35 na Kundin Tsarin Mulki, yana mai cewa dokar ACJA ta tanadi damar tsare wanda ake bincike a kansa bisa umarnin kotu.
Ya ce, neman kotu ta bayar da beli a irin wannan yanayi tamkar gayyatar kotun ce ta zama kotun ɗaukaka ƙara kan hukuncin wata kotu mai matsayi iri ɗaya, abin da doka ba ta amince da shi ba.
Saboda haka, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar belin, inda Malami ya ci gaba da zama a hannun EFCC har zuwa kammala binciken da ake yi a kansa.
