Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince da sunayen mutane 64 da aka naɗa a matsayin jakadu, bayan ta yi la’akari da rahoton Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar.
A zaman da aka gudanar, Shugaban Kwamitin Harkokin Waje, Sanata Sani Bello, ne ya gabatar da rahoton tantancewar, inda majalisar ta amince da shawarwarin kwamitin baki ɗaya.
Sai dai a yayin zaman, Sanata Sahabi Yau ya yi tsokaci kan rashin sunan kowanne ɗan jihar Zamfara a cikin jerin sunayen da aka gabatar. Ya buƙaci majalisar ta sanar da Shugaban ƙasa game da wannan giɓi, domin a gyara.
Shugaban Majalisar Dattawa ya amsa wannan ƙorafi, inda ya bayyana cewa jerin sunayen da aka amince da su a halin yanzu ba su kammala duka ba.
Ya tabbatar wa sanatoci cewa zai miƙa wannan batu ga Shugaban ƙasa, tare da jaddada cewa za a sake turo wasu sunaye nan gaba, kuma Zamfara ba za ta kasance a baya ba.
A ranar 4 ga Disamba, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa da buƙatar tabbatar da jakadu 65, waɗanda suka ƙunshi jakadu 34 na aikin diflomasiyya da kuma 31 na siyasa da manyan kwamishinoni. Wasiƙar buƙatar ta karantu a zauren Majalisar Dattawa.
Jerin sunayen na siyasa ya ƙunshi fitattun mutane da dama a fagen siyasa da mulki, ciki har da tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta ƙasa, Mahmood Yakubu; tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode; tsohon Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu; da tsohon mataimakin shugaban ƙasa a fannin yaɗa labarai, Reno Omokri.
Sauran sunayen sun haɗa da Sanata Ita Enang, tsohon Gwamnan Jihar Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, Chioma Ohakim, Bello Danbazau, ɓice Admiral Ibok Ete (mai ritaya), da Sanata Jimoh Ibrahim, da sauransu.
An miƙa jerin sunayen ga Kwamitin Harkokin Waje na Majalisar domin gudanar da tantancewa, inda aka kammala aikin kafin amincewa da su a zauren Majalisar.
Tun da farko, an riga an tantance da amince da wasu mutane uku – Kayode Are, Aminu Dalhatu da Ayodele Oke – lamarin da ya kai jimillar sunayen jakadun da majalisar ta duba zuwa 68.
Naɗawar ta janyo martani daga ɓangarori daban-daban, inda wasu suka nuna damuwa kan halayen wasu daga cikin waɗanda aka naɗa. Tsohon Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Waje, Joe Keshi, ya ce wasu daga cikinsu bai kamata su kasance a aikin diflomasiyya ba ta kowanne ma’auni.
Haka zalika, Shugaban ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya, Afam Osigwe, ya soki yadda ‘yan majalisa suka gudanar da tantancewar cikin gaggawa ba tare da zurfin tambayoyi ba.
Sai dai Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Harkokin Waje da Tsari, Ademola Oshodi, ya kare naɗin, yana mai cewa mutanen da aka zaɓa su ne mafi dacewa da muradun gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma ci gaban Nijeriya.
