Daga MARYAM BATOOL
A Arewa, kaya ba kawai rufe jiki kawai suke ba, suna bayyana al’ada, martaba da kwaliyya. Daga rigar zane ta gargajiya irin su saki, tsamiya, bunu, fatari da sauransu, har zuwa kayan zamani masu salo, ɗinki da salon kaya sun kasance wani muhimmin ɓangare na rayuwa a Arewa. Wannan rubutun zai duba yadda tarihin ɗinki da salon kaya ya sauya daga ƙarni zuwa ƙarni, da kuma yadda matasa ke ɗaukar wannan sana’a da kuma sabunta ta a yau.
Asalin ɗinki a Arewa:
Shigowar Musulunci ya kawo sauye-sauye a tsarin kaya, inda aka fi karkata zuwa sutura masu rufe jiki da nuna ladabi, sabanin wasu tsoffin tsare-tsare da suka fi bude jiki ko bayyanar da wasu sassa.
Bayan haka kuma tun kafin zuwan Turawa, mutanen Arewa na ɗinki da hannu, suna amfani da auduga da aka nika da hannu domin dinka kayan da suka dace da yanayin su da al’adunsu. Maza na sa Taguwa, yar shara, babbar riga da wando, mata kuma na sa atampa, zani, taguwa, facala wato dankwali duk an shirya su da ɗinki mai kyan gani da alamar kamala.
A garuruwan kamar Kano, Zaria, da Katsina, akwai manyan guraren ɗinki da aka san su tun tarihi. Misali, unguwar Kofar Mata da Kofar Wambai a Kano sun shahara wajen sana’ar ɗinki da sayar da kaya.
Salon Kaya na Gargajiya
Salon kaya a da yana da tsari ne da ke nuna matakin mutum a cikin al’umma. Babban riga da hula suna wakiltar dattako da girmamawa; mata kuma na sa zani da gyale masu launi da ado, wanda ke nuna kima da ladabi.
Ana amfani da launuka masu ma’ana, kamar farin kaya don nuna tsabta da addini, jajaye da ruwan kasa don al’ada, da baki ko ruwan dorawa a wuraren zaman majalisa ko shagulgula. Akwai kuma ado da ake yi da zare kamar “Aska” da ke kara kima ga tufafi.
Chanji da tasirin zamani:
Bayan zuwan Turawa da ci gaban zamani, an fara ganin sauyi a tsarin ɗinki. Makarantun koyon ɗinki suka yawaita, injin ɗinki ya maye gurbin ɗinki da hannu, sannan kuma aka fara haɗa salon gargajiya da na Turawa.
Matasan Arewa da sabbin dabaru:
Yanzu haka, matasa da dama na koyon ɗinki domin suna ganin dama da darajar da ke cikin sana’ar. Suna bude shagunansu, suna amfani da kafafun yada zumunta wajen tallata kayayyakinsu, kuma suna halartar taruka da gasar ɗinki domin nuna fasahar su da kwarewa kamar “Arewa Fashion Week” da sauransu.
Manya maza da mata na canza tunanin cewa ɗinki sana’ar ‘yan mata ce kawai. Maza da dama yanzu na ɗinki, suna amfani da kayan su wajen bayyana ra’ayinsu, kalar su, ko addininsu.
A yanzu haka kullum matasa suna cikin kirkire kirkire da kawo sababbin dinkuna da suka da ce da mata da maza na wannan zamani, kama daga dogayen riguna da ake amfani da su kampala, adire, atampa da materiyal na zamani. Da kuma dinkunan Maza da shararun masu ɗinki kamar Wambal, AZ teɗtiles da sauransu ke zagayawa garuruwa da ketare.
Mata ma ba abar su a baya ba, akwai su Bintaberry, Malaabis by Maymz, Adorable Cuts da sauransu, da suke ɗinkin zamani da na Amare da yan mata, sannan kuma sunan koyar da ɗinkin shi kansa.
Kyautata sana’ar ɗinki:
Sana’ar ɗinki ba wai kawai kayan sawa kadai take samarwa ba,tana raya al’ada, tana ba matasa sana’a, kuma tana taimaka wa tattalin arzikinmu.
ɗinki a Arewa ya zarce rufin jiki, salo ne, tarihi ne, kuma alama ce ta ƙwarewa.
