Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da kammala biyan wani tsohon bashi da ya daɗe yana jiran warwarewa, inda gwamnatin jihar ta raba sama da Naira biliyan 8.2 a matsayin ragowar alawus-alawus ga tsofaffin kansiloli 1,371.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.
Biyan kuɗaɗen ya nuna nasarar kammala wani shiri mai matakai uku da gwamnatin ta kirkiro domin biyan dukkan hakkokin sallama da suka hada da garatuti, alawus na kayan ɗaki, masauki, da hutun aiki, ga kansilolin da suka yi aiki tsakanin shekarun 2014 zuwa 2024.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan mataki ba wai biyan kuɗi kaɗai ba ne, illa mayar da mutunci, amana da adalci ga waɗanda suka yi wa al’umma hidima.
Ya tunatar da alƙawarin da ya ɗauka a watan Agustan 2025 na kammala biyan bashin kafin ƙarshen watan Disamba, inda ya ce: “Wannan magana ba kalamai ne na siyasa kawai ba, alkawari ne na gaskiya da aka gina bisa jajircewa da tausayi.”
Gwamnan ya yi bayani kan yadda aka aiwatar da shirin mataki-mataki: an fara da biyan Naira biliyan 1.8 ga tsofaffin kansiloli 903 da suka yi aiki daga 2014 zuwa 2017 a watan Mayu; sai kashi na biyu na Naira biliyan 5.6 da aka biya ga mutane 1,198 da suka yi aiki daga 2018 zuwa 2020 a watan Agusta; sannan kuma aka kammala da wannan “babban mataki na karshe” na Naira biliyan 8.26 ga wadanda suka yi aiki daga 2021 zuwa 2024. Jimilla, gwamnatin jihar ta biya Naira biliyan 15.67 domin warware wannan tarihi na bashi.
Haka kuma, gwamnan ya sanar da cewa kansilolin da ke kan aiki a yanzu, wadanda wa’adinsu ya fara a shekarar 2024, sun samu kashi 50 cikin 100 na alawus din kayan daki, wanda ya kai Naira biliyan 1.27, domin tabbatar da adalci da daidaito.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa ma’aikatun gwamnati da hukumomin da suka shiga aikin bisa tabbatar da gaskiya da bayyananniyar hanya wajen aiwatar da shirin, tare da godewa ƙungiyar Tsofaffin Kansiloli bisa haɗin kai da fahimta.
