Gwamnatin Jigawa za ta kashe Naira biliyan 17 don inganta lafiyar dabbobi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce ta ware sama da Naira biliyan 17 domin inganta lafiya da rayuwar dabbobi a faɗin jihar.

Kwamishinan kula da harkokin dabbobi na jihar, Farfesa Abdulrahman Salim, ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kare kasafin kuɗin da ma’aikatar na shekarar 2026 a gaban kwamitin noma da kiwo na majalisar dokokin jihar a Dutse.

Farfesa Salim ya ce za a yi amfani da kudin wajen gudanar da ayyuka daban-daban da ma’aikatar ta mayar da hankali kan su domin inganta rayuwar dabbobi a shekarar 2026.

Ya ce ma’aikatar ta gabatar da shirin kafa wuraren kiwon dabbobi a fadin jihar, inda za a girke makiyaya da sauran masu kiwon dabbobi.

A cewarsa, waɗannan wuraren kiwo za su ƙunshi abinci mai inganci ga dabbobi, makarantu masu kyau ga ’ya’yan makiyaya, cibiyoyin kiwon lafiya, asibitocin dabbobi, wutar lantarki da kuma samar da ruwan sha.

Farfesa Salim ya ƙara da cewa wannan shiri zai taimaka wajen rage rikice-rikicen da ke faruwa tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Kwamishinan ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen kafa asibitocin dabbobi a dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar, asibitoci bakwai na shiyya da kuma babban asibitin dabbobi na jiha wanda zai zama cibiyar ba da shawara.

Ya bayyana cewa suna da ƙwararrun likitocin dabbobi, sai dai matsakaita da ƙananan ma’aikata suna buƙatar sake horarwa.

Haka kuma, ma’aikatar ta ba da shawarar farfaɗo da cibiyoyin kiwon dabbobi guda uku da ke ƙananan hukumomin Gumel, Birniwa da Kaugama, inda ya ce an riga an fara aiki a wasu daga cikin cibiyoyin.

By ukarofi