Yau Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin 2026  

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da ƙudirin Kasafin Kuɗin 2026 ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Tarayya a yau Juma’a da misalin ƙarfe 2:00 na rana. 

Ofishin Magatakardar Majalisar Tarayya ya sanar da cewa za a takaita shiga harabar majalisar tun daga ƙarfe 11:00 na safe saboda dalilan tsaro.

Ana hasashen kasafin kuɗin 2026 zai kai Naira tiriliyan 54.4, bisa Tsarin Kashe Kuɗi na Matsakaicin Lokaci (MTEF) da Takardar Tsarin Kuɗi (FSP) na 2026–2028.

A wani mataki daban, Shugaba Tinubu ya nemi Majalisar Tarayya da ta soke tare da sake kafa Dokar Kasafin Kuɗin 2024, ta hanyar kudirin Appropriation (Repeal and Re-enactment Bill 2) 2024, wanda ya kai jimillar Naira tiriliyan 43.56.

Shugaban ƙasa ya ce ƙudirin na da nufin kawo ƙarshen gudanar da kasafi fiye da ɗaya a lokaci guda, tare da ƙarfafa tsari, gaskiya da ɗaukar alhaki a harkar kuɗaɗen gwamnati. 

An riga an miƙa ƙudirin zuwa Kwamitin Kasafi na Majalisar Wakilai domin ci gaba da aiki a kai.

Masana dai sun yi gargaɗin cewa tsawaita kasafi na iya haifar da ruɗani da matsaloli wajen aiwatar da ayyuka da kuma rage amincewar masu zuba jari.

By ukarofi