Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, ta amince da rahoton likita da takardar shaidar mutuwar tsohon hadimin shugaban ƙasa, Ahmed Gulak, a matsayin shaida a ci gaba da shari’ar da ake yi wa Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar ƙungiyar Biyafara ta IPOB, wanda ke fuskantar tuhume-tuhume na ta’addanci.
Mai shari’a James Omotoso, wanda ya jagoranci zaman shari’ar, ya amince da takardun da masu gabatar da ƙara suka gabatar ta hannun wani mai bada shaida a matsayin BBB, bayan babu wata adawa daga tawagar masu kare wanda ake hukuma, Kanu Agabi (SAN), tare da Chukwuma-Machukwu Ume (SAN) da Aloy Ejimakor.
Lauya mai shigar da ƙara, ƙarƙashin jagorancin Adegboyega Awomolo (SAN), ya gabatar da takardun da suka haɗa da rahoton ‘yan sanda daga Owerri, jihar Imo, da ke alaƙanta mutuwar Gulak da ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ƙungiyar IPOB ne.
A yayin amsa tambayoyi, Agabi ya ƙalubalanci sahihanci da cikar bayanin faifan bidiyo da aka samu na Kanu daga hannun hukumar DSS, inda ya bayyana cewa wanda ake ƙara da tawagarsa ne kawai ake gani a faifan.
Shaidan ya amsa, “Wannan ita kaɗai bidiyon,” yana mai tabbatar da cewa shi ne cikakken bidiyon. Lokacin da aka ƙara matsawa, ya kasa tunawa ko ya sanya abin rufe fuska yayin hirar.
Agabi ya nuna damuwa game da tsawaita tsare Kanu da kuma zargin zaman kaɗaici.
Sai dai shaidan ya ci gaba da cewa, shi mai bincike ne kawai kuma ba shi da alhakin tsare Kanu ko jin daɗinsa, yana mai cewa: “Ajiye mutum a zaman kaɗaici ba al’adar DSS ba ce, ni ba mai kula da shi ba ne.”
Lauyan ya ƙara da nuna shakku kan sahihancin tsarewar da aka daɗe ana yi, inda ya ce hakan ya kasance mummunan cin zarafi, amma shaidan ya dage cewa bai san halin da Kanu ke ciki ba, kuma ya ce hakan ba ya cikin aikinsa na bincike.
A ci gaba da bincike, shadan ya ce, ba shi da hannu wajen tsara tuhume-tuhumen kuma bai san ranakun da aka yi wa waɗanda ake tuhumar kwaskwarimar wasu laifuffuka ba.
Agabi ya tabbatar da cewa tuhume-tuhumen hasashe ne, yayin da shaidan ya sake nanata cewa aikinsa bincike ne kaɗai.
A wani al’amari mai ban mamaki, an shaida wa kotun cewa duk da gyare-gyare da aka yi a takardar tuhumar tsawon shekaru da dama, jami’in binciken bai yi ido biyu da Kanu ba.
Shaidan ya ce kawai ya gabatar da wata takarda daga babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) ne amma bai yi haɗuwar fuska da fuska ba.
Dangane da buƙatar neman wasu muhimman takardu, Agabi ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake karewa sun nemi wasu bayanan ‘yan sanda amma har yanzu ba su samu ba. Yayin da Awomolo ya ƙi amincewa da ɗage shari’ar, bisa dalilin umarnin da kotu ta bayar na a gaggauta sauraren ƙarar, Mai shari’a Omotoso ya amince da ɗage zaman na ɗan lokaci kaɗan.
Kafin a ɗage zaman, Mai shari’a Omotoso ya nemi ƙarin haske game da ikirarin zargin hukumar DSS ta hana lauyoyin Kanu su gana da shi.
Yayin da Kanu Agabi (SAN) ya musanta cewa an hana shi shiga wurin Kanu, kotun ta nuna damuwarta kan yadda wani lauyan Kanu, Aloy Ejimakor ya wallafa wani bidiyo a shafukan sada zumunta wanda ya janyo muhawara.
Alƙalin ya ja kunnen Ejimakor kan rashin ɗa’a, sannan ya buƙaci dukkanin lauyoyin da su riaa tantance bayanai kafin su wallafa su musamman a shafukan sada zumunta.
A halin da ake ciki, kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga watan Mayu a gaban lauyoyin ke kare wanda ake hukuma.
